Home Labarai Gwamnati ta kori ma’aikatan jinya 16,000 da suka shiga yajin aiki

Gwamnati ta kori ma’aikatan jinya 16,000 da suka shiga yajin aiki

0
Gwamnati ta kori ma’aikatan jinya 16,000 da suka shiga yajin aiki

Daga Hassan Y.A. Malik

Akalla ma’aiakatan jinya16,000 da ke aiki a asibitocin gwamnati ne suka gamu da sallama daga aiki bayan da suka shiga yajin aiki sakamakon kin biyansu albashi na tsawon watanni da gwamnati ta yi.

Sai dai mataimakin shugaban kasar Zimbabwe, Constantino Chiwenga ya zargi ma’aikatan na jinya da cewa yajin aikijn nasu na da alaka da siyasa, inda ya ce za su saka musu da sallama daga aiki tare da dauko marasa aiki a layin da ma ma’aikatan jinya wadanda suka bar aiki don su maye gurbinsu.

Kungiyar ma’aikatan jinya ta Zimbabwe mai suna Zimbabwe Nurses Association (ZINA), ta ce ta baiwa gwamnati da hukumar lafiya ta kasar zuwa karfe 2:00 na rana na ranar Alhamis mai zuwa da su dawo da wadanda suka kora a bakin aikinsu ko kuma su fuskanci gurfana a gaban kuliya.

Mataimakin shugaban kasar ya ce kungiyar ZINA ta ki karbar dalar Amurka miliyan 17 don biyansu wasu daga cikin basussukan albashi da gwamnati ke binsu.

Kungiyar malamai ta kasar, wacce ita ma ke shirin shiga yajin aiki a wata mai zuwa ta gargadi gwamnati da ta janye wannan hukunci na sallamar ma’aikatan jinyar, haka suma kungiyoyin likitoci da na lauyoyi sun yi Allah wadai da wannan hukunci.

Shugaban kasa Emmerson Mnangagwa, wanda ya canji Robert Mugabe a watan Nuwamban 2017 zai tsaya takarar shugaban kasa a watan Yulin shekarar nan, inda zai kara da Nelson Chamisa na jam’iyyar Movement for Democratic Change party mai shekaru 40.

A lokacin da Mnangagwa ya karbi mulki daga Mugabe, ya yi alkawari kawo sauyi game da tabarbarewar tattalin arzikin kasar tare da cin hanci da rashawa da ya samu gindin zama a kasar na tsawon lokaci. Har yanzu dai rashin aikin yi a Zimbabwe ya kai kaso 80 cikin 100, inda ma’aikata ke shan bakar wahala kafin su samu albashinsu.