Home Siyasa PDP ta ragewa matasa ƴan shekaru 25-30 kudin fom ɗin takara

PDP ta ragewa matasa ƴan shekaru 25-30 kudin fom ɗin takara

0
PDP ta ragewa matasa ƴan shekaru 25-30 kudin fom ɗin takara

 

Uwar Jam’iyyar PDP ta kasa ta bayyana cewar ta ragewa matasa ‘yan shekaru 25 zuwa 30 kudin fom din shiga zabe da kashi hamsin cikin dari.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cewar ta domin baiwa matasa damar shigowa a dama da su a cikin harkokin gwamnati.

Idan ba a manta ba an zabi matashi dan shekaru 26 Muhammad Kadade Sulaiman a matsayin shugaban matasan jamiyyar na kasa, wanda hakan ya nuna da gaske Jam’iyyar take wajen ganin ana damawa da matasa a sha’anin jamiyya da kuma shugabanci a Najeriya.

Da yake nuna jin dadinsa kan wannan batu. Zababben shugaban matasan Jam’iyyar Muhammad Kadade yace dole su jinjinawa taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ya amince da wannan sabon tsari.

A saboda haka, Kadade yayi kira ga matasa da su zo a dama da su ci gajiyar wannan sabon tsari a cikin Jam’iyyar PDP wajen ganin sun tsaya takarkaru a mukamai da dama da ya kamata a dama su a harkar gudanar da mulki a Najeriya.