
Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC ta mayar da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano da ga Legas.
A yammacin Alhamis ɗin nan ne dai EFCC ta damƙe Obiano ɗin a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
A cewar sahfin yanar gizo na Channels TV, an kama Obiano ɗin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare a yau.
Obiano, wanda a jiya rigar kariyar sa daga kame ta ƙare, ya kasance a cikin jerin sunayen waɗanda EFCC ɗin ke fako, in ji Wilson Uwujiaren, Kakakin hukumar.
Ya ce a yau juma’a ne a ka tafi da Obiano din zuwa shelkwatar EFCC ɗin da ke Abuja.
Kakakin ya ce EFCC ta samu nasarar cafke Obiano ne bayan ta nemi bayanan motsin sa da ƙoƙarin da ya ke na ficewa da ga ƙasar daga filin jirgin sama ko wasu wuraren da zai iya ficewa.
Sai dai kuma har yanzu EFCC ɗin ba ta fitar da bayanai a kan laifukan tsohon gwamnan ba.