
Wata mata mai suna Hajiya Hauwa Mai-kitso da ke zaune a unguwar Kadawa da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano ta koka kan cewa gobara ta addabe ta.
Duk da har yanzu ba a san da ga ina matsalar ta ke ba, amma al’umma sun fara hasashen cewa ko aljanin nan mai suna Batoyi ne ke haɗa mata gobarar, duba da cewa wutar ce ka tashi ba tare da wani musabbabi ba.
Da ta ke zanta wa da tashar Rahma Radio a Kano, Hajiya Hauwa ta ce sau goma sha biyar kenan wutar na tashi, inda ta ce ko ta kai kayan nata wani gida, sai wutar ta bi su can ta ƙone su.
A cewar ta, ta yi iya bakin ƙoƙarin ta, kuma gashi duk kuɗaɗen ta da kayan ta sun ƙare.
Cikin alhini da damuwa, Hajiya Hauwa ta ce “ga marayu ina tare da su. Ni ce cin su, ni ce shan su, suma kayan su duk sun ƙone. Koma irin kwancen kayan nan da al’ummar Annabi su ke taimaka mana da su, su ma sai ƙone wa su ke yi
“Na rasa inda zan saka kai na. Ina dai ta addu’a. Wasu sun ce ko aljanin Batoyi ne, to ni dai Allah ne masani.
“Ina dai rokon taimakon al’umma da a kawo min ɗauki dan Allah dan Annabi,” in ji Hajiya Hauwa.