
Uwar Jam’iyar PDP ta ƙasa ta ce har yanzu ba ta tsaida matsaya a kan ko wanne ɓangare ne na ƙasar nan zai fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa ba.
Ta ce ta yanke shawar fara sayar da fom ɗin takara ne domin kada ta saɓa wa wa’adin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa Mai Zaman Kanta, INEC ta sanya.
Shugabancin jam’iyar ya ce sabo da jadawalin da INEC ta fitar, shi ya sanya ba a hana kowa ya sayi fom ba, musamman ma Abubakar Atiku da Sanata Rabi’u Kwankwaso.
A tuna cewa tuni Atiku ya sayi fom ɗin takara, wanda kuɗin da ya kai Naira miliyan 400, inda ya ce wata kungiyar ƴan kasuwa a Arewa ce ta sai masa.
Bayan Atiku da Kwankwaso, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ma na neman takarar shugabancin kasar a jam’iyar adawa ta PDP.
Hakazalika gwamnonin PDP na shiyyar kudu sun bi sahun ƴancuwan su na APC wajen tsaya wa a kan cewa dole ɗan takarar shugabancin kasa daga ɓangaren su zai fito.