Home Siyasa Babban Taron APC: Modu Sheriff ya fice da ga tseren neman shugabancin jami’ya

Babban Taron APC: Modu Sheriff ya fice da ga tseren neman shugabancin jami’ya

0
Babban Taron APC: Modu Sheriff ya fice da ga tseren neman shugabancin jami’ya

 

 

Yayin da jam’iya mai mulki ta ƙasa, APC ke tunkarar babban taron ta a ranar Asabar mai zuwa, tsohon gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya fice da ga tseren neman shugabancin jam’iyar.

A wata hira da yayi da manema labarai a yau Lahadi a Abuja, Sheriff ya ce ya ajiye burin nashi ne saboda tsaron da jam’iya ta fitar na cewa daga Arewa-ts-Tsakiya za a bada shugabancin jam’iyar.

Amma kuma Sheriff, wanda ya fito da ga Arewa-maso-Gabas, ya ce zai dawo cikin tseren idan har APC ta canja ra’ayi da ga nan zuwa Juma’a.