Home Labarai Lauya ya maka wanda ya ke karewa a kotu sabo da ƙin biyansa N100,000 kuɗin aiki

Lauya ya maka wanda ya ke karewa a kotu sabo da ƙin biyansa N100,000 kuɗin aiki

0
Lauya ya maka wanda ya ke karewa a kotu sabo da ƙin biyansa N100,000 kuɗin aiki

 

 

 

Wani kamfanin lauyoyi a Jihar Kaduna mai suna Moonlight Attorneys ya kai ƙarar wani Yusha’a Abdullahi zuwa kotun Shari’ar Muslunci a bisa ƙin biyan kamfanin kuɗin aikin da ya yi masa har Naira dubu 100.

Lauyan mai ƙara, Atiku Abdulra’uf ya shaida wa kotun cewa wanda a ke ƙara ya nemi mai ƙara da ya kare shi a kotu, inda su ka daddale a kan naira dubu 100 a matsayin kuɗin aiki.

Ya ƙara da cewa tuni kamfanin ya riga ya yi masa aikin da ya buƙata, amma kuma wanda a ke ƙara ya ki biyan kuɗin aikin duk da irin bibiya da magiya da a ke yi masa, shi ya sanya kamfanin ya kawo shi kotu domin ta kwatar masa hakkinsa.

A nashi ɓangaren, wanda a ke ƙara ya ce ya san da adadin kuɗin da kamfanin ya yanka masa amma ya nemi ragi, inda ya ƙara da cewa ya na da niyyar ya biya da zarar an yi masa ragin.

Sai dai kuma alkalin kotun, Malam Nuhu Falalu ya ce dole wanda a ke ƙara sai ya biya dubu 100 ba tare da an masa ragin a tunda tun asali an daddale da shi a kan haka, inda ya umarce shi da ya biya kuɗin kafin ko a ranar 4 ga watan Afrilu.

Ya kuma umarci a ci gaba da tsare shi a kotun har sai ya kawo mutane 2 da za su tsaya masa sannan a bada belin sa.