Home Ilimi JAMB za ta rufe yin rijistar jarrabawar UTME/DE 2022 a ranar 26 ga Maris

JAMB za ta rufe yin rijistar jarrabawar UTME/DE 2022 a ranar 26 ga Maris

0
JAMB za ta rufe yin rijistar jarrabawar UTME/DE 2022 a ranar 26 ga Maris

 

Hukumar shirya Jarrabawar shiga Makarantun gaba da Sakandare, JAMB ta jaddada matakin rufe yin rijistar jarrabawar a ranar Asabar, 26 ga watan Maris.

Hukumar ta sanar da haka ne a yau Litinin a Abuja a mujallar mako-mako da ofishin Babban Rijistara ke fitar wa.

A cewar JAMB, a ranar 26 ga Maris ɗin za ta rufe sayar da katin yanar gizo na rijistar Haɗaɗɗiyar Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare, UTME da kuma na shiga Makarantun Gaba da Sakandare kai Tsaye, DE.

“Mun ɗauki wannan matakin ne sabo da yadda mu ke ganin yadda a ke sayar da katinan yanar gizo ke ƙaruwa amma kuma ɗaliban da ke zuwa cibiyoyin jarrabawar na raguwa.

“Za a iya tuna cewa hukumar JAMB ta ce ba za ta tsawaita wa’adin yin rijistar da hukumomin da su ke saman ta su ka bata ba.

“Sabo da haka duk wadanda su ke da sha’awar yin rijistar su hanyarta su je su yi kafin ranar rufewar,” in ji mujallar.

Hukumar ta ce a halin yanzu ɗalibai 1, 512, 739 su ka yi rijista da ga ranar 29 ga Maris.