Home Siyasa Ƴan takarar shugaban ƙasa 15 ne a jam’iyar mu — NNPP

Ƴan takarar shugaban ƙasa 15 ne a jam’iyar mu — NNPP

0
Ƴan takarar shugaban ƙasa 15 ne a jam’iyar mu — NNPP

 

Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyar NNPP, Ambasada Agbo Major, ya baiyana cewa yanzu haka a kwai ƴan takarar shugaban ƙasa guda 15 a jam’iyar.

Ya kuma ƙara da cewa akwai ƴan takarar gwamna, da na ƴan majalisu da dama a jam’iyar.

Da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja a yau Talata, Major ya ce jam’iyar za ta yi babban taron ta na shiyyoyi a ranar 28 ga watan Maris.

Ya ƙara da cewa a ranar 30 ga Maris kuma NNPP za ta yi babban taron ta na kasa a Abuja, inda za ta zabi shugabannin jam’iyar na din-din-din.

Major ya ƙara da cewa NNPP ta fito ne domin ƙwatar mulki a hannun APC don ta kawo gyara a ƙasar nan sakamakon lalace wa da ta yi a hannun jam’iyar mai mulki.

Ya ƙara da cewa dubban al’umma ne, musamman matasa ke shigo wa NNPP, inda ya ce jam’iyar a shirye ta ke ta baiwa duk wani ɗan ta dama.