Home Siyasa Idan na ci zaɓe, zan zama kamar gada tsakanin mulkin dattawa da matasa – Atiku Abubakar

Idan na ci zaɓe, zan zama kamar gada tsakanin mulkin dattawa da matasa – Atiku Abubakar

0
Idan na ci zaɓe, zan zama kamar gada tsakanin mulkin dattawa da matasa – Atiku Abubakar

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da takarar neman shugabancin ƙasar a babban zaɓe na 2023 mai zuwa a jam’iyyar adawa ta PDP.

Atiku, wanda ya shafe shekara fiye da 15 da su ka wuce ya na neman shugabancin Nijeriya, ya ce zai mayar da hankali kan ɓangare uku idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Da ya ke jawabi ya yin taron a yau Laraba a Abuja, Atiku ya ce gwamnatinsa za ta zama gada tsakanin mulkin dattijai da na matasa idan ya ci zaɓe a 2023.

“Gwamnatinmu za ta zama kamar gada ce [da za ta haɗa] tsakanin mulkin dattijai da na matasa.”

Ya ci gaba da cewa: “A ƙarƙashin mulkina, zan mayar da hankali kan ɓangare biyar masu muhimmanci; haɗin kan Najeriya, tsaro, tattalin arziki, ilimi, ciyar da ɓangarorin gwamnatin tarayya gaba da ƙara musu iko.”