
Yayin da a ke tunkarar babban taron jam’iyar APC, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Gwamnonin APC sun amince da fitar da shugaban jam’iya ta hanyar yarjejeniya.
A taron da su ka yi a jiya Laraba a fadar shugaban kasa, Buhari ya nuna wa gwamnonin ra’ayinsa na zabar tsohon gwamnan Jihar Nassarawa, Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jami’ya na ƙasa.
Gwamnonin kuma sun amince da zaɓinsa.
An zaɓi tsohon shugaban nahiyar dattijai, Ken Nnami a matsayin mataimakinsa da ga shiyyar Kudu.
Sai kuma Abubakar Kyari, a ka zaɓe shi a matsayin mataimakin shugaban jami’ya na yarjejeniya, ɓangaren Arewa.
Wani gwamna ya shaida wa manema labarai cewa an amince da a fitar da mataimakin shugaban jami’ya ɓangaren Arewa daga shiyyar Arewa-maso-Gabas, shine a ka zaɓi Kyari.