
Ƙungiyar Izala ta kasa ta yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya buɗe rumbunan abinci da kuma rage farashi domin al’umma su ji saukin lamura a watan Ramadan.
Shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Laune ya yi wannan kira a jiya lokacin buɗe Masallacin Juma’a na ƙungiyar a Abuja.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Lau ya ce an gina Masallacin ne da kuɗin fatar da jama’a suka bayar a lokacin layya.
Sheikh Bala Lau ya ce ya shaida wa shugaba Buhari wanda ya halarci bikin buɗe Masallacin cewa ya kamata gwamnatinsa ta sa ido ta tabbatar da ba a tsawwala farashin kayayyaki ba.