
Jami’an tsaro sun cafke wasu mutum uku da ake zargi da yankan aljihu a wajen babban taron jam’iyar APC da ke gudana a Abuja, bayan kama su suna satar wayar salula a kofar shiga filin taron.
Wani jami’in tsaro ya faɗa wa kamfanin labarai na Najeriya NAN cewa waɗanda aka Kama ɗin sun faki idon dandazon mutane da ke kofar shiga filin taron na Eagle Square wajen sace wayoyinsu.
Jami’in tsaron ya kuma ce waɗanda ake zargi da sace wayoyin sun haɗa baki wajen aiki tare, inda suke sace wayoyi da kuma kuɗin mutane da ke filin taron.
Har wa yau, jami’in tsaron ya ce an samu damar kama mutanen ne da taimakon sauran abokan aikinsu ‘yan sanda da ke sanya ido a kofar shiga Eagle Square yayin da wakilai ke shiga domin kaɗa kuri’arsu.
Ya ce za a kai waɗanda ake zargin zuwa shelikwatar ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.