Home Ƙasashen waje Ghana ta buɗe bodojinta na ruwa da na ƙasa bayan shekaru biyu da kulle wa

Ghana ta buɗe bodojinta na ruwa da na ƙasa bayan shekaru biyu da kulle wa

0
Ghana ta buɗe bodojinta na ruwa da na ƙasa bayan shekaru biyu da kulle wa

 

Shugaban Ƙasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya bada umarnin buɗe illahirin bodojin ƙasar na ruwa da na ƙasa, bayan ya kulle su shekaru biyu da su ka gabata.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tun a ranar 21 ga watan Maris, 2020 ne Akufo-Addo ya bada umarnin kulle illahirin bodojin ƙasar a wani mataki na daƙile yawaitar yaɗuwar cutar korona.

Sai dai kuma, a taron bada bayanai a kan annobar korona, karo na 28 a jiya Lahadi a birnin Accra, Akufo-Addo ya sanar da sake buɗe bodojin, inda ya ce umarnin ya zo ne biyo bayan sauƙi da a ka samu wajen yaɗuwar cutar s ƙasar.

A cewar sa, bayan buɗe dukkanin bodojin, mutane za su iya wuce wa zuwa wasu ƙasashen ko shigo wa daga wasu ƙasashen matsawar mutum ya yi alluran rigakafin korona guda biyu.

Tuni dai wannan mataki ya sanya murna da farin ciki ga ƴan ƙasar, inda su ke ganin hakan zai farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

A cewar wani direba, “kulle bodojin ya matuƙar gurgunta tattalin arzikinmu. Mu direbobi ne da mu ke jigilar kayaiyaki zuwa ƙasashe maƙwabta, rufe bodojin nan ya tsaida harkokin mu cak.

“Duk ga motocin namu nan mun ajiye su duk sun yi ƙura sabo da ba harka. Amma yanzu, alhamdulillah, mun ji daɗi sosai. Za mu ci gaba da harkokin mu, mu ci gaba da samun abinda za mu baiwa iyali,” in ji shi.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a yau Litinin ne dai za a buɗe bodojin ƙasar na ruwa da na ƙasa, inda za a ci gaba da kula da zirga-zirgar mutane ta hanyar bin dokokin kariya da ga kamuwa da cutar korona.