
An tsinci wani yaro da bai wuce shekara 6 da haihuwa ba, wanda ya baiyana sunansa da suna Muhammadu da a ka turo shi almajiranci a Jihar Kano.
Yaron ya baiyana ne a jiya a wani faifen bidiyo da wani shararren ɗan jarida, Nasiru Salisu Zango ya wallafa a shafinsa na facebook yayin da ya ke yi masa tambayoyi a jiya Lahadi.
A bidiyon, an baiyana cewa an ga yaron ne ya na ta gararamba a gari ba tare da ya san inda za shi ba, shine wasu bayin Allah su ka kai shi wajen wani Hussaini, wanda ɗan uwan Mai Unguwar Ƙofar Mata a nan Jihar Kano.
Muhammadu ya baiyana cewa mahaifinsa ya kawo shi bara ne Kano daga garin Gamawa da ke Jihar Bauchi bayan mahaifiyarsa ta rasu.
Tabubbukan duka kuma ya ce malamin makarantar allon su ne ya ke dukan sa idan bai kawo masa abinci idan ya je bara ba.
Sai dai kuma biyo bayan wallafa bidiyon da Zango ya yi, mahaifin yaron ya nemo lambar wayarsa ya kuma kira shi Zangon.
A cewar mahaifin, kamar yadda Zango ya sake wallafa wa a shafinsa na facebook,
kakar yaron ce ta matsa masa lamba kan sai ya bayar dashi an tafi almajirancin domin malamin ɗan ta ne,
“mahaifin yace shima yayi karatun allo amma bai taba zuwa ko ina domin yin bara ba.
“Ya tabbatar da cewar mahaifiyar yaron ta rasu, Kuma shi a iya sanin sa ba a gaya masa Kano za a tafi da dan sa ba, domin malamin ya gaya masa cewar Gaidam zai je dashi.
“Yanzu haka mun yi dashi zai Zo Kano a gobe Talata da safe domin karbar dan sa.ya kuma bayyana takaici bisa irin mugun dukan da ya ga an yiwa ɗan nasa,” in ji Zango.
Sai dai kuma wani Lauya mai kare hakkin ɗan adam, Barista Abba Hikima, ya ci alwashin sai an nemo malamin yaron an hukunta shi a bisa zaluntar yaron da ya yi.
A cewar Hikima, sai malamin ya biya yaron diyya sakamakon cin zarafin sa da ya yi kamar yadda doka ta tanada.