
Hukumar kula da Asibitoci ta Jihar Kano, KSHMB ta ƙaryata rahotannin cewa ƴan daba sun kai hari sashen agajin gaggawa na Asibitin Murtala Mohammed a Jihar Kano.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ranar Alhamis ne rahotanni su ka baiyana cewa cikin dare yan daba, ɗauke da muggan makamai sun farwa masu jiyya da marasa lafiya, inda su ka ƙwace musu wayoyi da kuɗaɗe.
Sai dai kuma a wata sanarwa da kakakin hukumar, Ibrahim Abdullahi ya fitar a yau ya ƙaryata harin, inda ya ce babu wata cikakkiyar hujja cewa an kai harin.
A cewar sa, bayanan da hukumar ta samu shine, ƴan vigilante ne su ka biyo wasu barayi da misalin ƙarfe 3 na dare, shine su ka biyo ta kofar asibitin yayin da su ke neman wajen ɓuya.
Ya ƙara da cewa mutanen da ke wajen asibitin, da su ka hango ƴan daban na gudu, shine su ma su ka tsere.
“Wannan shine abinda ya faru. Amma babu wani hari nanƴan daban a cikin asibitin.
“Amma abin takaici, sai ga rahotanni sun fito cewa wai an kai hari cikin asibitin.
“Asibitin Murtala yana da girman gaske kuma yana ɗaukar daruruwan jama’a, sabo da haka jami’an tsaron asibitin ba lako-lako ba ne. Ban da jami’an tsaron da hukumar asibitin ke ɗauka aiki, akwai caji-ofis na ƴan sanda a ciki,” in ji Abdullahi.