Home Labarai Tinubu ya soke bikin tunawa da ranar haihuwarsa sabo da harin jirgin ƙasa

Tinubu ya soke bikin tunawa da ranar haihuwarsa sabo da harin jirgin ƙasa

0
Tinubu ya soke bikin tunawa da ranar haihuwarsa sabo da harin jirgin ƙasa

 

Jagoran Jam’iyar APC na Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya soke biki na musamman na tunawa da ranar haihuwarsa karo na 13 domin jimamin waɗanda harin jirgin ƙasa ya shafa a jiya Litinin.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa Tinubu ya sanar da soke bikin ne mintinan kaɗan kafin a soma.

Tinubu ya siffanta harin da bala’i a ƙasa.

Ya ce “na damu matuƙa a kan lamarin kuma abu ne da ya ke bukatar a yi duba na tsanaki,”

An rawaito cewa tuni manyan baƙi su ka hallara a wajen kafin ya sanar da sokewar.