
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya sauka a filin Asibitin rundunar sojoji ta 44 domin duba waɗanda su ka ji raunuka a harin jirgin ƙasan da ƴan ta’adda su ka kai a jiya Litinin.
An kwantar da wasu da ga cikin waɗanda abin ya shafa a Asibitin Sojojin, inda wasu kuma a ka kai su St. Gerald a Jihar Kaduna.
Tun da fari, Gwamna Nasir El-rufa’i na Jihar Kaduna ne ya fara ziyartas waɗanda abin ya shafa a asibitin.
Daga bisani kuma sai Osinbajo ya zo, inda ya gana da El-rufa’i, kafin da ga bisani ya je ya ga marasa lafiyar.