Home Ƙasashen waje Shugaban Sudan ya kori shugabannin jami’o’in kasar

Shugaban Sudan ya kori shugabannin jami’o’in kasar

0
Shugaban Sudan ya kori shugabannin jami’o’in kasar

 

Jagoran sojojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya nada sabbin shugabannin jami’o’in kasar 30.

Ya dauki matakin ne bayan ya yi amfani da wata dokar soja inda ya ruguza kwamitin amintattu na jami’o’in.

Tun watan Oktoban 2021 yake amfani da dokar soja bayan sun kawar da gwamnatin rikon-kwarya da Firaminista Abdallah Hamdok yake jagoranta.

Farfesoshi a Jami’ar Sudan University sun ce za su soma yajin aiki domin birjirewa wannan mataki, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Kamfanin ya ambato shugaban jami’ar Khartoum yana bayyana matakin Janar Burhan a matsayin wanda bai halasta ba.

Jami’o’i da makarantu na cikin ‘yan gaba-gaba a zanga-zangar da ake yi domin kyamar mulkin sojin Sudan.