
Ƴan ta’adda da su ka kai hari kan jirgin ƙasa a kan hanyar sa ta zuwa Kaduna da ga Abuja a ranar Litinin sun fara tuntuɓar iyalan fasinjojin da su ka yi garkuwa da su.
Iyalin wani da ga cikin fasinjojin da ya ke hannun ƴan ta’addan, mai suna Abdullahi, sun ce ƴan fashin dajin sun tuntube su ta wayar salula kuma sun ce musu su shirya biyan kuɗin fansa.
Punch ta rawaito cewa wani Jibreel Khalil, ɗan uwan Abdullahi ɗin ya ce duk da ba su fadi nawa za a basu ba, amma dai ƴan ta’addan sun kira sun kuma ce yana hannun su sannan a shirya biyan kuɗaɗen fansa.