
A yau Alhamis ne wata Kotun Majistare da ke Abeokuta ta yanke wa wani makiyayi mai suna Abdullahi Adamu mai shekaru 38 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin zamba da satar shanun da suka kai sama da Naira miliyan 43.
Adamu, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, an same shi da laifuka uku da suka haɗa da haɗin-baki, zamba da kuma sata.
Da take yanke hukuncin, mai shari’a Olajumoke Somefun, ta ce dukkanin shaidun da masu gabatar da kara su ka gabatar sun tabbatar da cewa babu tantams wanda a ke tuhuma ya aikata laifin.
Somefun ta bayyana cewa bayan an samu wanda ake ƙara da laifi kamar yadda ake tuhumarsa, amma ta yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari tare da zaɓin biyan tarar N250,000.
Ta ƙara da cewa tarar za ta yi aiki ne idan wanda a ka ya ke wa hukuncin ya dawo dawo da shanu 259 ɗin da ya sace.
Tun da fari dai, ɗan sanda mai shigar da kara, ASP Olakunle Shonibare, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Satumba a kauyen Alamutu ta hanyar Rounder, a Abeokuta.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, ASP Olakunle Shonibare, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Satumba a kauyen Alamutu ta hanyar Rounder, a Abeokuta.
Shonibare ya ce wanda aka yankewa hukuncin ya hada baki da wani mutum guda, wanda a halin yanzu ya gudu, su ka sace shanu 259 na mutane bakwai.
Ya ce wanda aka yankewa hukuncin makiyayi ne kuma a na bashi shanun mutane ya kiwata.
Mai gabatar da ƙara ya ce Adamu, da niyyar damfara, sai ya karbi shanun da niyyar kiwata wa amma sai ya mayar da su nashi na kansa da nufin ya hana masu shi.
Haka kuma, wanda aka yanke wa hukuncin ya kwashe shanu 15 da kudinsu ya kai Naira miliyan 1.5, da kadarar Funmilayo Ogunlana, da shanu 12 da darajarsu ta kai Naira miliyan 1.2, mallakin Jimoh Salaudeen.
Ya kuma saci shanu biyar, wanda kudinsu ya kai N500,000, na Adekunle Adedolapo, da shanu shida, na Kabiru Bankola, N600,000, da shanu biyu, wanda darajarsa ta kai N200,000, mallakar Abeebi Adeyemi.
Mista Shonibare ya lura cewa jimillar duk shanun da wanda aka yankewa laifin ya sace ya kai Naira miliyan 43.9.
A cewar mai gabatar da kara, laifukan da aka aikata sun ci karo da sashe na 516, 383 da 390 (3) (6) (a) na kundin dokokin jihar Ogun, 2006.