
Kasar Saudiyya ta sanar da ganin watan Ramadan na Shekarar 1443 a yau Juma’a .
Hakan na nuni da cewa gobe Asabar za a fara azumin watan Ramadan ɗin a ƙasa mai tsarki.
Kafar yada labarai ta Haramain Sharifain da ke Saudiyya ce ta sanar da hakan a Sahihan shafukanta na Facebook da Twitter.
Hakazalika Daily Nigerian Hausa ta tuntuɓi wasu ƴan Nijeriya da ke zaune a Saudiya, inda su ka tabbatar da cewa an sanar da ganin watant a ƙasar.
A yau Juma’a ce 29 ga watan Sha’aban kuma ita ce ranar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad ya bada umarnin a fara duban watan na Ramadan a Nijeriya.