
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar adawa ta PDP da su haɗa kansu gabanin zaɓukan 2023, in dai jam’iyyar na son samun nasara.
Yero, wanda yayi wannan kiran a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a jiya Lahadi a Kaduna, ya ce PDP na iya rasa zaɓen idan mambobin basu haɗa kan su ba.
Ya ce ya zama dole ga mambobin jam’iyyar su haɗa kan su domin samun nasarar zaɓe mai zuwa a ƙasar.
Ya ce “yana da mahimmanci ga ƴan PDP dasu haɗa kan su domin ceto Najeriya.
“Dole mu goge duk wani rashin jituwa tare da ajiye Son kai a gefe, tare da yin dubi akan abinda ƴan Najeriya ke so da Jam’iyyar.
“Idan Nijeriya ta zama Ƙasa mai ikon kanta, dukkanin mu zamu ji daɗi, kuma zamu yi farin ciki da yanayin.
“Idan muka cigaba da yin faɗa da juna, muka inganta son kanmu, zamu ƙare a rasawa.”
Yero ya kuma yi kira ga matasa da su yi amfani da lokacin zaɓen 2023 tare da gina kansu a matsayin su na shuwagabannin gobe.