
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya amince da nadin Usman Bala Muhammad a matsayin sabon Shugaban Ma’aikata, wanda har zuwa sabon nadin nasa, ya kasance Babban Sakatare a Ma’aikatar Yaɗa Labarai.
Sannan Gwamnan ya amince da nadin Muhammad Bello Shehu a matsayin Babban Sakatare a Hukumar Kula da Tituna ta Jiha, wanda har zuwa wannan sabon nadin ya kasance Daraktan Bincike da Kididdiga ne na Hukumar.
Ganduje ya kuma naɗa Magaji Lawan, wanda shi ma har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin Babban Sakatare, ya kasance Darakta ne na kula da Asusun Gwamnati na Ma’aikatar Kudi, Bilyaminu Gambo Zubairu wanda kuma shi ne Darakta na PHC na shiyyar Rano, yanzu ya zama sabon Babban Sakatare a hukumar.
Mairo Audi Dambatta, wacce har zuwa sabon nadin nata, ta kasance Darakta a ofishin shugaban ma’aikata, yanzu ta zama Babbar Sakatare a ofishin.
Ganduje ya ce dukkannin naɗe-naɗen muƙaman za su fara aiki ne da gaggawa.
A yayin da yake taya su murna kan sabbin ayyukan da aka ba su, Gwamna Ganduje ya hore su da su yi aiki tukuru domin inganta kyawawan halaye a aikin gwamnati.
Ya kara da cewa, “Dole ne ku ɗauke shi a zaman wani ɓangare na ayyukan ku, yin amfani da dabarun fasahar zamani a cikin ayyukan ku na yau da kullun.
“Dole ne ku kuma ku tuna cewa, ingantattun bayanan tarihin ku a aikin gwamnati ne su ka ba ku damar kaiwa ga wannan matsayi. Don haka duk idanu za su kasance a kan ku don ganin yadda za ku yi ayyukan ku,” in ji Ganduje.