
Kotun Ɗaukaka Ƙara a Jihar Kano a yau Laraba ta yi watsi da hukuncin da wata babbar Kotun Tarayya ta Kano ta yanke, wanda ta wanke Abdulsalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da A. A Zaura.
Daily Nigerian Hausa ta tuno cewa Hukumar yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta Ƙasa, EFCC ce ta gurfanar da A. A Zaura, mai neman takarar gwamna a jam’iyar APC a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano bisa tuhume-tuhume biyar.
Hukumar ta zargi Zaura da damfarar wani ɗan kasar Kuwait kuɗi $1,320,000 bisa zargin cewa yana sana’ar gine-gine a Dubai da Kuwait da sauran ƙasashen Larabawa.
A ranar 9 ga Yuni, 2020, Mai shari’a Lewis Allagoa ya sami wanda ake tuhuma ba shi da laifi kuma ya sallame shi kan dukkan tuhume-tuhumen.
A bisa rashin gamsuwa da hukuncin da karamar kotun ta yanke, Lauyan da ke kare masu kara Musa Isah ya shigar da ƙarar a kotun ɗaukaka ƙara a wani yunƙuri na soke hukuncin da karamar kotun ta yanke.
A wani mataki na bai daya da wasu alƙalan kotun ɗaukaka ƙarar guda uku suka yanke kuma mai shari’a Abdullahi M. Bayero ya sanar da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.
Bayero ya bayar da umarnin a sake yi wa wanda ake ƙara shari’a bisa jagorancin wani alkali na daban ba Justice Allagoa ba.
Babban abin da ake ta cece-kuce a cikin ɗaukaka ƙarar shi ne wanda ake tuhuma bai halarci kotun ba a lokacin da aka yanke hukuncin kuma bisa wasu hukunce-hukuncen da kotun kolin ta yanke, an ce wanda ake tuhuma dole ne ya kasance a gaban kotu a duk tsawon shari’ar da ake yi masa ciki har da yanke hukunci.
A kan haka ne kotun ɗaukaka ƙara ta samu ikon karɓa tare da yin watsi da hukuncin baya.
“Bayan an tantance batun don goyon bayan wanda ya shigar da ƙara, a dabi’ance karar ta yi nasara, An soke ƙarar mai lamba FHCK/CR2018/FRN wadda aka shigar kan Abdulsalam Sale Abdulkarim wanda aka yanke hukuncin ranar 9 ga watan Yuni, 2020.”
Bayero ya kuma bayar da umarnin a mayar da shari’ar zuwa babbar kotun tarayya a sake fara shari’ar.