
Ƙungiyar Ma’aikatan da Ɓangaren Koyarwa ba na Jami’o’i, NASU da takwararta ta Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya, SSANU, sun ce za su tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani idan har gwamnati ta gaza biya musu bukatunsu.
Kungiyoyin da ke karkashin Kwamitin hlHadin gwiwa, JAC ne suka bayyana hakan ta bakin kakakinta, Prince Adeyemi, yayin wani taron manema labarai a jiya Laraba a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya tuna cewa mambobin kungiyar sun shiga yajin aikin gargadi na makwanni biyu, wanda ya kare a tsakar daren ranar 10 ga watan Afrilu.
Bukatun kungiyar sun haɗa da rashin daidaiton biyan albashi na sabon tsarin albashi na bai-ɗaya, IPPIS, rashin biyan kudaden alawus-alawus, rashin biyan bashin mafi karancin albashi na kasa da kuma ƙarin da a ka samu.
Sauran buƙatun sun haɗa da: rashin baiwa jami’o’i kuɗaɗen gudanarwa, jinkirin sake tattaunawa kan yarjejeniyoyin 2009, rashin samar da tsari a bangarorin ziyara, rashin biyan kudaden ritaya ga mambobin da suka kammala aiki, da dai sauransu.
Mista Adeyemi, ya ba da sharuɗɗan da za a iya dakatar da ayyukansu na masana’antu.
Ya nace cewa yakamata gwamnati ta yi watsi da IPPIS don Tsarin Ma’aikata na Jami’ar da tsarin biyan albashi wanda ƙungiyoyin da ba na ilimi suka kirkira ba.