
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce kawo yanzu ta raba sama da Naira miliyan 600 ga mata ƴan kasuwa ta hanyar asusun tallafawa mata da aka fara a shekarar 2018.
Kwamishiniyar Aiyuka da ci gaban Al’umma, Hafsat Baba ce ta bayyana hakan a wata tattaunawa da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Alhamis a Kaduna.
Baba ta ce an bayar da tallafin ne ga ƙungiyoyin mata ƴan kasuwa a faɗin jihar a matsayin lamuni mai sauƙi.
Ta ce an ƙaddamar da asusun ne domin bunƙasa ƙanana da matsakaitan masana’antu da kuma rage matsalolin wariyar jinsi a cikin harkokin kasuwanci.
“Har ila yau, don tallafa wa kasuwanci da kuma bunƙasa tattalin arzikin mata, wadanda suka riga sun shiga kasuwanci kuma za su iya amfani da su don kara yawan jari,” in ji ta.
Kwamishiniyar ta ce kungiyoyin haɗin gwiwa da kungiyoyin mata a karkara da birane za su iya samun bashi na tsakanin Naira 5,000 zuwa Naira miliyan 10 ba tare da lamuni ba, “domin samun kudaden da ake bukata sai ku bi ta banki domin gaskiya da rikon amana.
A cewar Mrs Baba, akasarin wadanda suka ci gajiyar tallafin na biyan bashin da suka karba.
Kwamishinan ya ce gwamnati ta sanya ido kan wadanda suka ci gajiyar shirin da kuma yadda suke gudanar da ayyukansu domin samun isassun labaran nasara da kuma koyan darasi.
A cewarta, ana ci gaba da bayar da lamunin na shekarar 2022.