Home Wasanni An farfasa motar Katsina United a wasan da su ka kara da Kano Pillars

An farfasa motar Katsina United a wasan da su ka kara da Kano Pillars

0
An farfasa motar Katsina United a wasan da su ka kara da Kano Pillars

 

Maimakon ta kasance rana ta fari ciki ga dubban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Sai Masu Gida, duba da cewa a yau ne ta dawo yin wasa a filin wasanta na Sani Abacha, da ke Kofar Mata a cikin birnin Kano.

Sai dai kuma jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a na tsaka da wasan ne sai magoya bayan Pillars su ka fara jifa kan mai-uwa-da-wabi cikin fili, inda daga bisani su ka danna cikin filin har sai da aka tsaya da wasan a mituna na 79 kuma wasan da ba a ci gaba ba kenan.

 

Su kan su ƴan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United ɗin da ƙyar su ka sha a hannun ƴan kallon.

Jami’an tsaro na ƴan sanda ne dai su ka samu nasarar shawo kan lamarin.

Amma kuma an farfasa motar kungiyar ƙwallon ƙafar ta Katsina.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa hakan ba ya rasa nasaba da irin harin da a ka kaiwa ƴan wasa da magoya bayan Kano Pillars ɗin a can Katsina a kakar wasanni ta 2020-2021, inda a jikkata magoya bayan Pillars da dama.

 

Lamarin da ya sanya mahukunta a Katsina United su ka yi tattaki zuwa Kano domin sansata wa.

Sai dai kuma Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars ta yi alla-wadai da abinda ta kira aikin ɓata-gari da magoya bayanta su ka yi a kararwar ta jiya.

A sanarwar da Kakakin Pillars ɗin, Lurwanu Malikawa Garu ya fitar a yau Lahadi, ƙungiyar ta ce ba ta yi tsammanin magoya bayanta za su yi wannan aika-aikar ba, duba da cewa ƙungiyar ta yi wasanni a cikin wasan na Muhammad Dikko da ke Katsina ba tare da wani tashin hankali ba.

Malikawa ya ce yanzu haka Pillars na jiran rahoton jami’an tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.

Ya kuma tabbatar da cewa babu wani daga cikin yan wasa da jagororin Katsina United da ya jikkata, inda ya ce an maida su gida a ɗaya da ga cikin motocin Pillars ɗin.