Home Siyasa Yari da Marafa sun fice daga APC zuwa PDP

Yari da Marafa sun fice daga APC zuwa PDP

0
Yari da Marafa sun fice daga APC zuwa PDP

 

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Marafa sun fice daga jam’iyyar APC, inda su ka koma jam’iyyar PDP.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, Bala Mande ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a karshen taron Kwamitin Ayyuka na jam’iyyar na Jiha a yau Lahadi a Gusau.

Ya ce nan ba da jimawa ba PDP za ta karbi Yari da Marafa da sauran manyan ƴan jam’iyyar APC da su ka sauya sheƙa tare da magoya bayansu.

“Mun kira ku ne domin mu yi muku bayani kan komawar babbar jam’iyyarmu ta PDP ta tsohon Gwamna, Mai Girma, Alhaji Abdul-Aziz Yari, Sanata Kabiru Garba Marafa da magoya bayansu.

“Sun shigo cikin mu, mun yarda kuma za mu aiwatar da yarjejeniyar.

“Mun amince da zama tare a jam’iyya daya wato PDP tare da hada kai domin samun nasarar jam’iyyar a jihar Zamfara.

Mande ya ce ‘ya’yan jam’iyyar PDP za su hada kai domin ganin sun lashe zaben 2023 a jihar.

A cewar sa, PDP za ta tarbi Yarinda sauran manyan ‘ya’yan jam’iyyar APC da sauka sauya sheka a hukumance a Gusau a ranar da ba a bayyana ba.