
Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan da takwaransa na Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila sun yi kira ga shugabancin jam’iyar APC da ya duba yiwuwar baiwa ƴan majalisun taraiyar da su ka yi ƙoƙari tikitin takara kai tsaye.
Shugabannin majalisun taraiyar sun yi wannan kira ne a taron ƙoki ma jam’iyar APC karo na 11 jiya Laraba a Abuja.
A cewar su, duba da irin jituwa da ke gsaka in ɓangaren majalisa da na shugaban ƙasa, ya na da kyau idan a ka baiwa ƴan majalisun kula wa ta musamman idan zaɓe ya zo
Kawan ya ce ya kamata jam’iyar ta gane cewa sun taka rawar gani a matsayin su na yan majalisu da kuma aiki cikin zaman lafiya da bangaren mulki da shatan shugabanni a gwamnati.
Ya ce duba da haka, yana kira ga uwar jam’iya da ta duba yiwuwar hakan, inda ya ƙara da cewa duk wanda ya taka rawar gani a majalisa to ya kamata a bashi kula wa ta musamman.