
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ta yi kira ga hukumomin tsaro, musamman na yaki da cin hanci da rashawa, da su gaggauta fara binciken duk masu neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da za su biya Naira miliyan 100 ko miliyan 50. don siyan fom ɗin takara.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwar da shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu ya fitar ta hannun Sakataren Yaɗa Labaran ta, Simon Imobo-Tswam.
“Wannan ma ai rashin tausayi ne daga jam’iyar mai mulki. A ce za a sayar da fom naira miliyan 100 da kuma miliyan 50, ya kamata a bincike duk wanda ya siya saboda sata ce wannan,”
PDP ta ce ta sayar da fom din kan kudi Naira miliyan 100 ga masu neman takarar shugaban kasa ya nuna cewa APC jam’iyya ce ta ƴan damfara.
Jam’iyyar PDP ta kayyade farashin fom din takarar shugaban kasa a kan Naira miliyan 40, kuma kawo yanzu ‘yan takara 17 ne suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takara.