
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, ya sha alwashin hanzarta kera makaman nukiliya tare da sanya su cikin shirin don fara amfani da su nan take.
Da yake magana a wajen faretin bikin cika shekaru 90 da kafa rundunar sojin kasar, Mista Kim ya yi gargadin shafe duk wata kasa da ke neman jan-zare da Pyongyang a kan wannan aniya.
BBC ta rawaito cewa hotunan da kafafen watsa labaran kasar suka wallafa sun nuna babban makami mai-linzamin kasar na Hwasong-17 wanda aka kammala gwajinsa a watan jiya, bayan tabbatar da cewa zai iya kai wa Amurka.
Wasu hotunan tauraron dan adam na baya-bayan nan sun nuna cewa ana ci gaba da aikin dawo da ramukan kera makaman da aka lalata a shekarar 2017 bayan Kim Jong-un ya tattauna da tsohon shugaban Amurka Donald Trump.