
Gwamnatin Jihar Zamfara ta sauke Sarkin Zurmi, Atiku Abubakar da na Dansadau, Hussaini Umar sakamakon zargin su da hannu a kashe-kashe da ƴan fashin daji ke yi a jihar.
A wata sanarwa da Kakakin Gwamna Bello Matawalle, Zailani Bappa ya sanya wa hannu, ya ce an kuma tsige Hakimin Birnin Tsaba, Sulaiman Ibrahim Danyabi.
Sanarwar ta bayyana cewa an yanke matakin ne a taron Majalisar Zartaswa ta jihar, ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin gwamnan jihar, Hassan Nasiha, kamar yadda Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ibrahim Dosara ya bayyana jin kaɗan bayan taron.
Sanarwar ta kara da cewa an yanke hukuncin ne bisa shawarwarin da kwamitin mutum shida su ka tattara daga sauran kwamitoci da gwamnatin ta kafa domin binciken zargin hannun sarakunan a kashe-kashe da ƴan fashin daji ke yi a jihar.
Sanarwar ta tuna cewa tun da fari a ka dakatar da sarakunan gargajiya ukun, bayan zarge-zarge masu ƙarfi s kan hannu da masu rike da masarautun su ke da shi a al’amuran ƴan ta’adda a jihar.
Hakazalika sanarwar ta ce kwamitocin sun gano badaƙalar filaye da sarakunan su ka yi, inda gwamnatin ta ƙwace filayen ta kuma bada umarnin a dakata kafin mataki na gaba.