
Wani sojan ƙasar nan, wanda a ka cafke shi ya na haɗa kai da ƴan ƙungiyar ƴan ta’adda ta ISWAP, ya harbe kansa a kan hanyar zuwa kai shi bariki.
Jaridar PRNigeria ta jiyo cewa sojojin da ke aiki a sashin binciken sirri ne su ka gano sojan, wanda ya ke aiki a wata bataliyar sojoji a Arewa-maso-Gabas, cewa yana da hannu a hare-haren da ISWAP ta kai kwanan nan a wuraren bauta da mashaya.
“Yana da hannu dumu-dumu a hare-haren da a ka kai a unguwanni a Geidam da Gashua a Jihar Yobe.
“Shine a ka cafke shi yayin da ya ke yunƙurin tsere wa bayan ya gano cewa an gane yana da alaƙa da ƴan ta’adda.
“Bayan an saka masa ankwa, kawai sai yayi amfani da ƙwarewa ya warci wata ƙaramar bindiga daga ɗaya da ga cikin sojojin da su ke raka shi, kawai sai ya harbe kan sa.
A halin yanzu an ci gaba da bincike domin nemo sauran ƴan ta’addan da su ka kai hare-haren,” inji wata majiya da ta shaida wa PRNigeria.