Home Labarai Al’ummar Mallam Fatori sun yi sallar idi shekaru 8 bayan Boko Haram ta kwace garin

Al’ummar Mallam Fatori sun yi sallar idi shekaru 8 bayan Boko Haram ta kwace garin

0
Al’ummar Mallam Fatori sun yi sallar idi shekaru 8 bayan Boko Haram ta kwace garin

 

A karon farko, al’ummar garin Mallam Fatori a Jihar Borno, sun gudanar da sallar idi ta bana, tun bayan da ƴan kungiyar Boko Haram su ka ƙwace garin a 2014.

PRNigeria ta gano cewa ƴan ta’addan ne su ka sanya al’ummar garin su ka tsere har tsawon shekaru 8.

Mallam Fatori, shelkwatar Ƙaramar Hukumar Abadam, ta yi iyaka da Nijar.

Binciken da PRNigeria ta gudanar ya baiyana cewa tun sanda sojoji su ka karɓe ikon garin Mallam Fatori daga hannun ƴan Boko Haram a 2015, sai da ƴan ta’addan su ka kai wa garin hari sojoji na tare wa har sau 300.

A irin wannan yaƙin ne na kare Mallam Fatori gwarzo sojan nan, Laftanal-Kanal Abu Ali ya rasa ransa a 2016.

Yanzu dai sojoji sun ƙwato garin an kuma kafa sansanin sojoji a garin.

Wani ma’aikacin jin-ƙai ya shaida wa PRNigeria cewa al’ummar garin na farin-cikin dawowar zaman lafiya a garin, sakamakon sojoji da su ka taka rawar gani da kuma tsarin tallafa wa ƴan gudun hijira na gwamnatin Borno.

“Ƴan watanni da su ka gabata duk mazauna garin sun dawo. Mun yi sallar idi kuma bayan nan mun sha bikin Sallah.

“Al’amura sun daidaita Yanzu a garin,” in ji shi.