
Hukumar KAROTA ta barranta kanta da wani da ake zaton jami’an ta ne da aka gani cikin wani bodiyo yayi mankas da giya.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Naisa ya fitar jiya Alhamis.
Kofar Naisa ya ce a binciken da Hukumar KAROTA ta gudanar ta tabbatar da cewa wanda ke jikin wannan bidiyo ba ma’aikacinta ba ne.
Haka kuma, Hukumar ta nuna rashin jin dadinta dangane da mummunan ta’adar da matashin ya nuna na yin amfani da kayan hukumar KAROTA duk da cewa ba ma’aikacinta ba ne.
Hukumar ta KAROTA ta miƙa shi hannun Hukumar Hisba ta jihar domin ɗaukar matakin Shari’a tare da gurfanar da shi a gaban Kotu.
Haka zalika Hukumar ta nuna jin dadinta dangane da an-karar da ita da wasu masu kishin jihar Kano suka yi a lokacin da suka ci karo da bidiyon.
A cewarsa hakan ne ya baiwa hukumar nasarar kamo shi tare da miƙa shi ga Hukumar Hisba domin daukar mataki na gaba.
Haka kuma shugaban Hukumar KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya godewa al’ummar jihar Kano waɗanda suka nuna rashin jin dadin su dangane da faruwar lamarin.