Home Siyasa Ƴan Majalisar Dokoki 9 sun sauya sheƙa zuwa NNPP a Kano

Ƴan Majalisar Dokoki 9 sun sauya sheƙa zuwa NNPP a Kano

0
Ƴan Majalisar Dokoki 9 sun sauya sheƙa zuwa NNPP a Kano

 

Ƴan Majalisar Dokoki 9 na Jam’iyyar PDP a zauren Majalisar Dokoki ta Jihar Kano sun sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar NNPP.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Majalisar, Uba Abdullahi ya fitar a yau Juma’a.

A cewar Abdullahi, ƴan Majalisar sun yanke shawarar sauya shekar zuwa NNPP ne sabo da rikicin da ya dabaibaye jam’iyar PDP a matakin jiha da na kasa baki ɗaya.

Ana sa bangaren shugaban Majalisar Dokoki ta Kano, engr Hamisu Ibrahim Chidari ya yi musu fatan alkairi.

Waɗanda su ka sauya sheƙar zuwa NNPP sun haɗa da;

1.Rt Hon. Isyaku Ali Danja Mai Wakiltar Karamar Hukumar Gezawa .

2.Hon. Umar Musa Gama, Dan Majalisa Mai Wakiltar Nassarawa.

3. Hon Aminu Sa’adu Ungogo, Mai Wakiltar Karamar Hukumar Ungogo.

4. Hon Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa. Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Dala.

5. Hon. Tukur Muhd Dan Majalisa mai Wakiltar Karamar Hukumar Fagge .

6. Hon.Mu’azzam El-Yakub, Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Dawakin Kudu .

7..Hon. Garba Shehu Fammar Dan Majalisa Mai Wakiltar Kibiya .

8.. Hon. Abubakar Uba Galadima, Dan Majalisa Mai Wakiltar Bebeji .

9.. Hon Mudassir Ibrahim Zawaciki, Dan Majalisa Mai Wakiltar Kumbotso .