Home Labarai Gwamnatin Taraiya za ta taimaka wa Anambra wajen magance matsalar tsaro — Osinbajo

Gwamnatin Taraiya za ta taimaka wa Anambra wajen magance matsalar tsaro — Osinbajo

0
Gwamnatin Taraiya za ta taimaka wa Anambra wajen magance matsalar tsaro — Osinbajo

 

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ya ce Gwamnatin Taraiya za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Gwamnatin Jihar Anambra domin magance matsalar tsaro a jihar.

Osinbajo ya faɗi hakan ne a wata gana wa da ya yi da gwamnan jihar, Chukwuma Soludo a garin Awka da ke Anambra a yau Juma’a.

Osinbajo, bayan ya ya suffanta Soludo a matsayin wata kadara ga ƙasa, ya nuna yakinin cewa Anambra za ta ci gaba a ƙarƙashin mulkin Soludo.

A cewar Osinbajo, Anambra ce jigon masana’antu a Nijeriya , musamman ƙanana da matsakaitan masana’antu.

Ya kuma ƙara da cewa jihar ta zama ɗaya daga cikin jihohi da su ka zama jigo wajen cigaban tattalin arziki.

“Tsaro abu ne mai muhimmanci, sabo da haka Gwamnatin Taraiya za ta haɗa kai da Gwamnatin Anambra domin dawo da doka da oda a jihar,” in ji Osinbajo.

A nashi ɓangaren, Soludo ya ce idan a ka samu haɗin gwiwa ingantacce tsakanin gwamnatin taraiya da ta Anambra tabbas za a samu a magance matsalar tsaro da ke damun jihar.