
Tsohon Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum ya fice da ga jam’iyar APC.
Rurum ya sanar da ficewar ta sa ne a wata tattaunawa da manema labarai ta wayar tarho a yau Lahadi, inda ya koka cewa ba a bin ƙa’idojin dimokaraɗiyya a jam’iyar.
Ya ce ya yi iya ƙoƙarin sa na ya ga an tabbatar da bin ƙa’idojin dimokaraɗiyya wajen fitar da ɗan takarar gwamna a jam’iyar amma hakan ya ci tira.
Shi ya sa ya ce ya fice da ga jam’iyar, inda ya kuma nuna cewa tuni ya fara tuntuɓar abokan harkar siyasar sa a kan jam’iyar da zai koma.
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa Rurum ya ɗauki wannan mataki ne bayan da a ke ta raɗe-raɗi mai ƙarfi cewa Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya zaɓi mataimakin sa, Nasiru Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamna, shi kuma Murtala Sule Garo, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, ya zama mataimaki a takarar.
Ƙarin bayani na nan tafe…