
Tsohon Shugaban Ƙasa, Jonathan Goodluck ya lale kuɗi wuri na gugar wuri har Naira miliyan 100 ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 a jam’iyar APC.
A wasu wasiku biyu ga Kwamitin Tsare-tsare na Ƙasa na jam’iyar, Bankin Heritage ya tabbatar da samun sanarwar shigar kuɗi Naira miliyan 100 na don ɗin takara.
A kwanan nan ne dai kungiyoyi da dama su ka riƙa kiraye-kiraye ga Jonathan da ya fito takararar shugaban ƙasa.