Home Kasuwanci Za a shiga wahalar man fetur da ba a taɓa ganin irin ta ba idan… — IPMAN

Za a shiga wahalar man fetur da ba a taɓa ganin irin ta ba idan… — IPMAN

0
Za a shiga wahalar man fetur da ba a taɓa ganin irin ta ba idan… — IPMAN

 

 

 

 

Ƙungiyar Dillalan Man fetur Mai zaman kanta ta Ƙasa, IPMAN ta yi gargaɗi cewa ƴan Nijeriya za su ga wahalar man fetur da ba a taɓa ganin irin ta ba a ƙasar in dai har hukumar mai ta NMDPRA ba ta biya su kuɗaɗen dakon mai ba.

Shugaban IPMAN shiyyar Kano, Bashir Ahmad Danmallam, shi ne ya yi wannan gargaɗi a taron manema labarai a Kano a jiya Litinin.

A cewar sa, rashin biyan kuɗin dakon, wanda a turance a ke kira ‘bridging claims’, wanda adadin sa ya haura Naira biliyan 500, ya sanya da yawa da ga cikin dillalan sun durƙushe.

Ya kara da cewa rashin biyan kuɗaɗen da NMDPRA ta yi ya sanya wasu ƴan ƙungiyar sun kasa ma dakon man zuwa jihohin ƙasar nan.

A cewar Danmallam, akwai isashshen mai a defo-defo a ƙasar nan, amma ƴan ƙungiyar ba za su ci gaba da dakon shi zuwa jihohi ba sabo da ƙin biyan su maƙudan kuɗaɗen da ba a yi ba kuma hakan, a cewar sa, ya yi wa kasuwancin su illa.

“Wasu fa bashi ma su ka ci na banki su ke harkar nan. Waɗan nan kuɗaɗen da mu muke tara su domin a samu daidaito wajen farashin man fetur yadda ƴan ƙasa za su samu sauki.

“Mu na da isashshen mai a ƙasa, amma ba za mu iya ci gaba da rarraba wa ba sabo da an ki biyan mu kuɗaɗen mu na dako.

“In dai ba a biya mu kuɗaɗen nan ba, to ƴan ƙasa su shirya ganin wahalar man fetur da ba a taba ganin irin ta ba,” in ji Danmallam.

Ya ƙara da cewa tun sanda a ka kafa NMDPRA a bara, sau biyu ta taɓa biyan su kuɗaɗen, inda ya koka cewa yanzu su na bin kuɗaɗen na wajen watanni 9.

Bayan ya yaba wa kamfanin mai na NNPC bisa ƙoƙarin tara isashshen man fetur, Danmallam ya yi kira ga gwamnatin taraiya da ta sanya NMDPRA ta biya su kuɗaɗen su domin kawo ƙarshen matsalar a ƙasa baki ɗaya.