
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya haramta gudanar da “zanga-zangar addini” game da batun ɓatanci da aka yi wa Annabi Muhammadu (SAW) a Jihar Sokoto.
Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Kaduna ta fitar a yau Asabar ta ce an ɗauki matakin “saboda yuƙurin wasu marasa kishin ƙasa” na shirya zanga-zangar adawa da kuma goyon bayan lamarin.
“An faɗa wa Gwamna El-Rufai halin da ake ciki kuma ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar da hana duk wani nau’i na zanga-zangar addini a jihar,” a cewar sanarwar da Kwamashinan Tsaro Samuel Aruwan ya sanya wa hannu.
Lamarin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu matasa su ka gudanar a Sokoto, suna masu neman jami’an tsaro su saki mutanen da suka kama bisa zargin kashe matashiyar nan Deborah Samuel da suka zarga da zagin Annabi.
Arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro ta jawo an harbi mutum biyu, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC Hausa.
Rahotanni sun ce zanga-zangar ta fara ne a matsayin ta lumana kafin ta rikiɗe zuwa jefe-jefe da duwatsu, inda su kuma jami’an tsaro suka mayar da martani da harbi da kuma hayaƙi mai sa hawaye.