
Wasu ƴan ta’adda da a ke zargin ƴan ISWAP ne da su ka kai harin bam a jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama sun sako wata fasinja mai juna-biyu, amma bisa tausaya wa.
A wani faifan bidiyo na musamman da jaridar DAILY NIGERIAN ta samu, matar (an sakaya sunanta) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tattauna da ƴan ta’addan domin ceto rayukan sauran da a ke tare da su.
Ta ce waɗanda suka yi garkuwa da su sun kula da su tare da ciyar da su abinci da basu magunguna.
Majiyar tsaro ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewa ba a biya kudin fansa ba wajen sako ta.
Majiyar ta kuma yi watsi da rahotannin kafafen yaɗa labarai na cewa mace ɗaya ta haihu a sansanin ƴan ta’addan.