
Rundunar haɗin gwiwa ta Multinational Joint Task Force, MNJTF, a jiya Asabar ta ce ta hallakamayakan Boko Haram da ISWAP 300, a yankin Arewa-maso-Gabas a tafkin Chadi.
Kamarudeen Adegoke, babban jami’in yada labarai na rundunar soji ta MNJTF N’Djamena, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri, ya ce an kashe ƴan ta’addar ne a arangama 30 daban-daban.
Adegoke, wanda ya ke da muƙamin Laftanar-Kanar, ya bayyana cewa, Kwamandan rundunar, Abdul Khalifa, ya bayyana haka a lokacin wani taro da daukacin kwamandojin MNJTF da aka zaɓo daga kowane bangare.
Khalifa ya ce an shirya taron ne domin yin nazari a ayyukan da aka riga a ka gudanar a halin yanzu domin shirye-shiryen tunkarar aiki na gaba.
A cewarsa, sama da ‘yan ta’adda 52,000 da suka hada da mayaka, wadanda aka maida su ƴan ta’adda ta karfi da yaji da kuma iyalansu sun mika wuya a yankunan da MNJTF da Op Hadin Kai da ke gudanar da ayyukansu.
Ya kuma yi kira ga ƴan ta’addan, da su ƴan Boko Haram ne ko kuma ISWAP ne, da su yi fita da ga wannan kungiyar ta masu aikata laifuka su kuma mika wuya kamar yadda dubban ƴan uwansu suka yi kafin lokaci ya ƙure musu.