Home Ƙasashen waje Ango, Amarya da baƙi 40 sun kamu da rashin lafiya bayan cin abincin biki

Ango, Amarya da baƙi 40 sun kamu da rashin lafiya bayan cin abincin biki

0
Ango, Amarya da baƙi 40 sun kamu da rashin lafiya bayan cin abincin biki

 

 

 

 

Sama da baƙi 40 da suka halarci bikin aure sun kamu da rashin lafiya sakamakon kamuwa da gubar abinci a abincin da su ka ci a lardin Takhar da ke arewacin ƙasar Afganistan, in ji ‘yan sanda a yau Litinin.

Wani jami’i danga rundunar ‘yan sandan lardin, Mubin Safi ya ce lamarin ya faru ne a yayin ɗaurin aure a ƙauyen Takhan Abad da ke gundumar Chah Hab a daren Lahadi.

Safi ya ce a cikin marasa lafiya har da ango da amarya.

Ya kara da cewa an kai mutanen da abin ya shafa asibitin gundumar inda da dama daga cikinsu suka samu kulawa a sashin kula da lafiya na cibiyar.

A cewarsa, an kama mutane uku biyo bayan lamarin sannan kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan gubar abincin da aka samu a gundumar.