
A kalla mutane huɗu ne su ka rasu bayan da tukunyar iskar gas ta fashe a unguwar Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano.
Da ya ke zanta wa da manema labarai a wajen da lamarin ya faru a safiyar yau Talata, Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar, Samaila Shuaibu Dikko ya tabbatar da cewa tukunyar gas ce ta fashe a shagon yin walda.
Ya ce fashewar wacce take mai nauyi ta shafi wani tsohon ginin wata makaranta, inda da wani gini s jikin sa, wanda ya fado wa mutane huɗu daga ciki su ka mutu.
Ya ce yanzu haka a na ci gaba da duba ƙuraguzan ginin domin ko za a gano wasu da ya danne.
Ya kuma ƙaryata raɗe-raɗin da a ke yi cewa fahdear bam ce, inda ya tabbatar da cewa tukunyar gas ce ta fashe.