Home Siyasa APC ta musanta cewa ta sauya jadawalin shirye-shiryen zaɓen 2023

APC ta musanta cewa ta sauya jadawalin shirye-shiryen zaɓen 2023

0
APC ta musanta cewa ta sauya jadawalin shirye-shiryen zaɓen 2023

 

Jam’iyyar APC ta buƙaci jama’a da su yi watsi da raɗe-raɗin da ake ta yaɗa wa cewa ta sauya jadawalinta shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2023 da ke zagaya wa a shafukan sada zumunta.

Felix Morka, Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar, a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Litinin, ya ce rahoton dangane da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar na bogi ne, kuma ya kamata a a yi watsi da shi.

“An ja hankalinmu kan wani labari da a ke yaɗa wa cewa jam’iyar mu ta taɓa jadawalin ayyuka da tsare-tsaren zaben 2023 a shafukan sada zumunta.

“Ya kamata a yi watsi da labarin a matsayin labaran karya,” in ji shi.

Ya kara da cewa jadawalin jam’iyyar da tsare-tsaren ayyukan shiga zaben 2023 ya kasance kamar yadda aka buga a baya.

Ya sake bayyana jadawalin da aka amince da shi kamar haka.

Zaɓen Gwamna- Juma’a, Mayu 20, 2022.

Zaɓen Majalisar Dokoki ta Jiha – Lahadi, 22 ga Mayu, 2022.

Zaɓen Majalisar Wakilai – Talata, Mayu 24, 2022.

Zaɓen Majalisar Dattawa – Laraba, Mayu 25, 2022.

Zaɓen Shugaban kasa – Litinin, Mayu 30th zuwa Yuni 1st, 2022.

Ya kara da cewa idan ya kama dole a yi wa jadawalin kwaskwarima, to za a sanar da irin wadannan sauye-sauye ta hanyoyin sadarwa na jam’iyyar ga jama’a.