Home Labarai Ƴan bindiga sun saki malamar makaranta a Kaduna, amma ƴarta da direbanta suna tsare

Ƴan bindiga sun saki malamar makaranta a Kaduna, amma ƴarta da direbanta suna tsare

0
Ƴan bindiga sun saki malamar makaranta a Kaduna, amma ƴarta da direbanta suna tsare

Malama a Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, Dakta Rahmatu Abarshi ta shaƙi iskar ƴanci daga hannun ƴan fashin jeji.

A tuna cewa a cikin watan azumin Ramadan ne dai ƴan fashin jejin su ka yi awon gaba da Malamar, tare da ƴarta, Ameera da direbanta, jim kaɗan bayan ta gama rarraba kayan tallafi ga mabuƙata a Kaduna.

Tijjani Ramalan, Shugaban gidan telebijin na Liberty, a yau Alhamis ya bayyana cewa an saki malamar, amma kuma ƴan fashin jejin na ci gaba da tsare ƴar tata da direbanta.

Sai dai kuma babu wani bayani a kan ko an biya kuɗin fansa wajen sakin malamar.