Home Labarai Kotu ta yanke wa ɗan ƙasar Denmark hukuncin kisa bisa kashe matarsa da ƴarsa

Kotu ta yanke wa ɗan ƙasar Denmark hukuncin kisa bisa kashe matarsa da ƴarsa

0
Kotu ta yanke wa ɗan ƙasar Denmark hukuncin kisa bisa kashe matarsa da ƴarsa

Wata Babbar Kotun a Jihar Legas ta yanke wa wani ɗan ƙasar Denmark, Peter Nielsen hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kashe matarsa ƴar Nijeriya da kuma ƴar su.

Mai Shari’a Bolanle Okikiolu Ighile, ya yanke wa Nielsen, ɗan shekaru 54 hukuncin ne bisa tuhume-tuhume na kisa guda biyu da gwamnatin jihar Legas ta shigar da ƙara a kai.

Sai alkalin ya yanke masa hukuncin kisa a kan duka tuhume-tuhume biyun.

Ana tuhumar dan kasar Denmark ɗin ne da kashe matarsa, Zainab wacce mawakiya ce, da kuma ƴarsu, Petra.

Gwamnatin Legas na tuhumar ɗan Denmark ɗin da kashe matarsa da ƴarsa ta hanyar shaƙe su da misalin ƙarfe 3:45 na safe a gida mai lamba 4 a Bella Vista Tower, da ke Banana Island a Ikoyi a Legas.

A ranar 13 ga watan Yuni 2018 a ka gurfanar da Nielsen ɗin.

Sai dai kuma ya musa tuhume-tuhume biyun da a ka yi masa da suka saɓa da sashi na 223 na dokar laifuffuka ta Jihar Legas ta 2015.