Home Siyasa 2023: Zan koma Sambisa na tare idan na zama shugaban ƙasa – Al Mustapha

2023: Zan koma Sambisa na tare idan na zama shugaban ƙasa – Al Mustapha

0
2023: Zan koma Sambisa na tare idan na zama shugaban ƙasa – Al Mustapha

 

Manjo Hamza Al Mustapha tsohon dogarin marigayi Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, ya ce idan ya zama shugaban ƙasar Nijeriya, zai kawo karshen rikicin Boko Haram da ya addabi ƙasar, cikin watanni shida.

Al-Mustapha, wanda ɗan takarar shugaban ƙasa ne a karkashin jam’iyar Action Alliance, AA, ya baiyana haka ne a wata hira da BBC Hausa da Vanguard ta saurara a Kaduna.

Ya ce zai koma da zama a dajin Sambisa da ke jihar Borno da ake yi wa kallon a matsayin cibiyar ƴan Boko Haram, inda zai dauki matakan da suka dace domin murkushe ƴan ta’addan.

Ya koka da cewa sojojin Nijeriya a yanzu ba su da kuzari sosai kuma ba su da cikakkiyar himma kamar da, sun riga sun zama kamar ƴan sanda kuma su ƴan sandan da a kee da su sun lalace suma.

Ya ce zai yi wa sojojin ƙasar nan garambawul a cikin waɗannan watanni shidan, wanda zai zama an yi musu atisaye mai tsauri amma wanda ya zama dole domin dawo da martabar sojojin Nijeriya kamar yadda aka san su a da.

A cewarsa, “Na rantse idan ba zai yiwu a fatattaki ƴan ta’adda cikin watanni shida ba, zan sauke dukkan waɗannan manyan jami’an tsaro daga mukaminsu, in mayar da su gida, za a gurfanar da su a gaban kuliya, kuma dole ne su dawo da kuɗaɗen da a ka basu domin zan yi bincike a kansu.

“Idan na zama shugaban kasa zan zauna a Sambisa, zan zauna a can a karshen mako, da kuma lokutan hutu na ga ko wani abu zai taba ni,” in ji shi.

Tsohon jami’in dogarin na Abacha ya bayyana cewa a shirye ya ke ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a 2023 a karkashin jam’iyar AA.

Ya ce lokaci ya yi da ya kamata ya taka rawar gani a fagen siyasa, inda ya ce kungiyoyin da suka ba shi gudummawar kudi suka saya masa fom din tsayawa takara, suka yanke shawarar wane dandalin siyasa zai tsaya takara.